23 Yuli 2019 - 04:50
Buhari Ya Ce: Bai Kamata A Dora Alhakin Tsare Zakzaky Akansa Ba

Shugaban kasar Nigeria Mohammadu buhari yace bai kamata a dora masa Alhakin ci gaba da tsare jagoran yan uwan musulimi shaikh Ibrahim Elzakzaki ba.

(ABNA24.com) Wata sanarwa da fadar shugaban kasa ya fitar ta bakin kakakin shugaban Nigeria Malam Garba shehu ya ce bai kamata a zargi shugaba Mohammadu Buharida ci gaba da tsare jagoran yan uwa musulmi shaikh Ibrahim Elzakzaki ba, ganin cewa batun har yanzu yana gaban kotu a jihar Kaduna ,

Har ila yau sanarwar ta ci gaba a cewa fadar gwamnatin Nigeria ta na kira ga magoya bayan jagoran yan uwa musulmi da su jira hukuncin kotun da take kaduna mai makon su ci gaba da abin da ya kira tada zaune tsaye, don haka gwamnatin ba za ta zuba ido tana kallo ana hawa kan tituna ana karyar dokokin kasa ba, kuma ta bukacesu da su dane hawa titnuna suna zagin shugaban kasa tare da yi masa fatan mutuwa ,

A gefe guda kuma Tashar talbijin din chanel TV a Nigeria ta nakalto Femi Falana babban lauyandake kare Shaikh Ibrahim Elzakzaki yana watsi da sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, inda ya bukaci gwamnati da ta bi umarnin kotu ta saki shaikh Ibrahim zakzaki kafin ta bukaci magoya bayansa da su dena taka doka..

Kimanin Shekaru 4 ke nan ana ci gaba da tsare da Shaikh El zakzaki duk da umarnin da kotu ta bayar na a sakeshi, wannan yasa yan uwan musulmi din suke gudanar da zanga zangar neman a sake shi tare da mai dakinsa, domin neman magani a kasashen waje.


/129